<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>435</hymn_number>
<title>Kada Zuciyarku Ta Ɓaci LW435</title>
<lyrics>[V1]
 1) Kada zuciyarku ta ɓaci
 In ji Yesu Kristi.

[V2]
 2) Gama za shi sama
 Za ya shirya wuri can.

[V3]
 3) Za ya sake zuwa
 Domin ya karɓe mu.

[V4]
 4) Mu shirya zukatanmu
 Domin ranar zuwansa.

[V5]
 5) Kai, mai bi a karkace
 Sai ka gyara zamanka.

[V6]
 6) Kau da duka tsafinka
 Idan kai mai bi ne.

[V7]
 7) Idan yau da tsafin nan
 Allah yana kishinsa.

[V8]
 8) Idan kana da laya
 Allah yana kishinsa.

[V9]
 9) Rabu da waɗannan duka
 Ko dogara ga Allah.

[V10]
 10) Sai ka fara bidan
 Mulkin Allah yanzu.

[V11]
 11) Domin ka sami rai
 Cikin Yesu Mai Ceto.

[V12]
 12) Za mu zamna can a sama
 Cikin gidan Allah.

[V13]
 13) Daɗin, daɗi za mu ji
 Can tsare da Yesu.

[V14]
 14) Murna, murna za mu yi
 Can a gidan Allah.</lyrics>
</song>